Mubarak A Isah
Sannunku da zuwa shafina! Sunana Mubarak A. Isah, wanda aka fi sani da Manager. Ni haifaffen karamar hukumar Wurno ne da ke Jihar Sokoto, Nijeriya, kuma mutumin Hausa ne na asali gaba da baya. Ni Content Creator ne kuma mai bada shawarwari da nasihomi domin gina al'umma. Bayan haka, ni kwararre ne a fannin daukar bidiyo (Videography), tsara hotuna, da sauran ayyukan fasahar zamani (digital media). Abubuwan da Na Kware a Kansu (Core Competencies & Qualities) • Bada Kwarin Gwiwa da Shawarwari: Bunkasa tunanin jama'a da samar da shawarwari masu ginawa a rayuwar yau da kullum. • Kwarewa a Daukar Bidiyo (Videography): Amfani da fasaha mai kyau wajen daukar bidiyoyi masu nagarta da inganci. • Jagoranci da Gudanarwa (Management Skills): Ilimin tsara aiki, tafiyar da al'umma, da bayar da jagoranci na gaskiya. • Hazaƙa da Sarrafa Tunani (Creativity & Innovation): Samar da sababbin dabarun kirkire-kirkire wajen gina abubuwan kallo da sauraro masu kayatarwa. • Sadarwa da Hulɗa da Jama'a: Kyakykyawar dabi'a ta asali wajen sauraron mutane da gina dangantaka mai mai kyau tsakanina da masu kallo ko abokan aiki. Manufata (My Mission) Manufata ita ce amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen isar da saƙonni masu tasiri, fadakarwa, da samar da ingantattun ayyukan bidiyo da fasaha da zasu taimaka wajen ciyar da al'umma gaba.
Nigeria

Photos
Videos
Resume
TV / Film
Hausa Motivational speaker • short • Leading • Content • Manager
Attributes
Appearance
Special Skills
This website was built with Built with ActorCV
Create yours